Littafi Mai Tsarki

Ayu 41:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. 'Yan kasuwa za su saye shi?Za su karkasa shi ga fatake?

7. Za ka iya huhhuda fatarsa da zaguna?Ko kuwa kansa da māsu?

8. In ka kama shi, ka daɗe kana tunawa da yaƙin da ba za ka ƙara marmarin yi ba!

9. Ba ma amfani a yi ƙoƙarin kama shi,Tunanin yin haka ma abin tsoro ne.

10. Ba wani mai zafin hali da zai kuskura ya tsokane shi.Wane ne wannan da zai iya tsayawa a gabana?

11. Wa ya ba ni har da zan biya shi?Dukan abin da yake cikin duniyan nan nawa ne.

12. “Ba zan yi shiru a kan zancen gaɓoɓinsa ba,Ko babban ƙarfinsa, ko kyan ƙirarsa.