Littafi Mai Tsarki

Ayu 41:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Zai ƙulla alkawari da kai,Cewa zai zama baranka har abada?

5. Za ka yi wasa da shi kamar yadda za ka yi da tsuntsu?Ko za ka ɗaure shi da tsarkiya domin barorinka mata?

6. 'Yan kasuwa za su saye shi?Za su karkasa shi ga fatake?

7. Za ka iya huhhuda fatarsa da zaguna?Ko kuwa kansa da māsu?