Littafi Mai Tsarki

Ayu 41:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kama kifi?Ko kuma ka iya zarge harshensa da igiya?

2. Ka iya sa wa hancinsa asirka?Ko ka iya huda muƙamuƙinsa da ƙugiya?

3. Zai ta yi maka godo?Zai yi maka magana da tattausar murya?

4. Zai ƙulla alkawari da kai,Cewa zai zama baranka har abada?

5. Za ka yi wasa da shi kamar yadda za ka yi da tsuntsu?Ko za ka ɗaure shi da tsarkiya domin barorinka mata?

6. 'Yan kasuwa za su saye shi?Za su karkasa shi ga fatake?

7. Za ka iya huhhuda fatarsa da zaguna?Ko kuwa kansa da māsu?

8. In ka kama shi, ka daɗe kana tunawa da yaƙin da ba za ka ƙara marmarin yi ba!

9. Ba ma amfani a yi ƙoƙarin kama shi,Tunanin yin haka ma abin tsoro ne.

10. Ba wani mai zafin hali da zai kuskura ya tsokane shi.Wane ne wannan da zai iya tsayawa a gabana?