Littafi Mai Tsarki

Ayu 10:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Na gaji da rayuwa,Ku ji ina fama da baƙin ciki.

2. Kada ka hukunta ni, ya Allah.Ka faɗa mini laifin da kake tuhumata da shi.

3. Daidai ne a gare ka ka yi mugunta?Ka wulakanta abin da kai da kanka ka yi?Sa'an nan ka yi murmushi saboda dabarun mugaye?

4. Yadda mutane suke duban abu, haka kake duba?

5. Kai ma ranka gajere ne kamar namu?

6. In haka ne, me ya sa kake bin diddigin dukan laifofina,Kana farautar dukan abin da na yi?

7. Ka sani, ba ni da laifi,Ka kuma sani, ba wanda zai cece ni daga gare ka.

8. “Da ikonka ne ka yi ni, ka siffata ni,Yanzu kuma da ikon nan naka ne za ka hallaka ni.

9. Ka tuna, ya Allah, kai ka halicce ni, da yumɓu kuwa ka yi ni.Za ka murtsuke ni ne, in kuma koma ƙura?

10. Kai ne ka ba mahaifina ƙarfin da zai haife ni,Kai ne ka sa na yi girma a cikin cikin mahaifiyata.

11. Kai ne ka siffata jikina da ƙasusuwa da jijiyoyi,Ka rufe ƙasusuwan da nama, naman kuma ka rufe da fata.