Littafi Mai Tsarki

A.m. 9:35-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Duk mutanen Lidda da na ƙasar Sarona kuwa suka gan shi, suka juyo ga Ubangiji.

36. A Yafa kuwa akwai wata mai bi, mai suna Tabita, wato Dokas ke nan. Matar nan kuwa lazimar aiki nagari ce, da kuma gudunmawa.

37. A lokacin nan ta yi rashin lafiya, ta mutu. Da suka yi mata wanka, suka shimfiɗe ta a kan bene.

38. Da yake Lidda kusa da yafa take, da masu bi suka ji Bitrus na can, suka aiki mutum biyu wurinsa, su roƙe shi ya zo wurinsu ba da jinkiri ba.

39. Sai Bitrus ya tashi ya tafi tare da su. Da ya iso suka kai shi benen. Dukan mata waɗanda mazansu suka mutu suka tsaya kusa da shi, suna kuka, suna nunnuna riguna da tufafi da Dokas ta yi musu tun suna tare.

40. Amma Bitrus ya fitar da su duka waje, ya durƙusa, ya yi addu'a. Ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe ido, da ta ga Bitrus, ta tashi zaune.

41. Ya kuwa miƙa mata hannu ya tashe ta. Sai ya kira tsarkaka da matan waɗanda mazansu suka mutu ya miƙa musu ita rayayyiya.

42. Labari ya bazu a dukan Yafa, mutane da yawa kuwa suka gaskata da Ubangiji.