Littafi Mai Tsarki

A.m. 9:22-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Sai Shawulu ya ƙara ƙarfafa, yana ta dama hankalin Yahudawan da suke zaune a Dimashƙu, yana tabbatarwa, cewa Yesu shi ne Almasihu.

23. Bayan an ɗan daɗe Yahudawa suka ƙulla shawara su kashe shi.

24. Amma Shawulu ya sami labarin makircinsu. Dare da rana suna fako a ƙofofin gari don su kashe shi,

25. amma da daddare almajiransa suka tafi da shi, suka zura shi ta wata taga a jikin garu cikin babban kwando.

26. Da ya zo Urushalima ya yi ƙoƙarin shiga cikin masu bi, amma duk suka ji tsoronsa, don ba su gaskata shi mai bi ba ne.

27. Amma Barnaba ya kama hannunsa ya kai shi wurin manzannin, ya gaya musu yadda Shawulu ya ga Ubangiji a hanya, da yadda Ubangiji ya yi masa magana, da kuma yadda ya yi wa'azi gabagaɗi da sunan Yesu a Dimashƙu.

28. Daga nan ya yi ta cuɗanya da su a Urushalima,

29. yana wa'azi gabagaɗi da sunan Ubangiji. Ya kuma riƙa magana da Yahudawa masu jin Helenanci, yana muhawwara da su, amma suka yi ta neman kashe shi.