Littafi Mai Tsarki

A.m. 28:17-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Bayan kwana uku ya kira manyan Yahudawan birnin. Da suka taru sai ya ce musu, “Ya ku 'yan'uwa, ko da yake ban yi wa jama'armu wani laifi ba, ko laifi a game da al'adun kakanninmu, duk da haka an bashe ni ɗaurarre ga Romawa tun daga Urushalima.

18. Su kuwa da suka tuhume ni, suna so su sake ni, don ban yi wani laifi da ya isa kisa ba.

19. Amma da Yahudawa suka ƙi yarda, sai ya zamar mini dole in nema a ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar, ba don ina ƙarar jama'armu ba ne.

20. Shi ya sa na nema in gana da ku, tun da yake dai saboda sa zuciyar nan da Isra'ila take yi ne nake ɗaure da sarƙan nan.”

21. Sai suka ce masa, “Mu kam, ba mu sami wata wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, ba kuwa wani ɗan'uwanmu da ya zo nan ya kawo labarinka, ko yă faɗi wata mummunar magana game da kai.

22. Amma muna so mu ji daga bakinka abin da yake ra'ayinka, don in dai ta ɗariƙar nan ne, mun sani ko'ina ana kushenta.”

23. Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa'an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.

24. Waɗansu sun rinjayu da maganarsa, amma waɗansu sun ƙi gaskatawa.

25. Da suka kasa yarda a junansu, kafin su watse sai Bulus ya yi musu magana ɗaya ya ce, “Ashe kuwa, Ruhu Mai Tsarki daidai ya faɗa, da ya yi wa kakanninku magana ta bakin Annabi Ishaya cewa,

26. ‘Je ka wurin jama'ar nan, ka ce,Za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba faufau,Za ku gani kuma, amma ba za ku gane ba faufau.

27. Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta,Sun toshe kunnuwansu,Sun kuma runtse idanunsu,Wai don kada su gani da idanunsu,Su kuma ji da kunnuwansu,Su kuma fahimta a zuciyarsu,Har su juyo gare ni in warkar da su.’

28. To, sai ku sani, wannan ceto na Allah, an aiko da shi har ga al'ummai, su kam za su saurara.”

29. (Da ya faɗi haka, sai Yahudawa suka tashi suna ta muhawwara da juna.)

30. Sai Bulus ya zauna a nan a gidan da yake haya, har shekara biyu cikakku, yana maraba da duk wanda ya je wurinsa,

31. yana ta wa'azin Mulkin Allah, da koyar da al'amarin Ubangiji Yesu Almasihu gabagaɗi, ba tare da wani hani ba.