Littafi Mai Tsarki

A.m. 28:11-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Bayan wata uku muka tashi a cikin wani jirgin Iskandariya, wanda ya ci damuna a nan tsibirin. An kuwa yi masa alama da surar Tagwaye Maza.

12. Da muka zo Sirakusa muka kwana uku a nan.

13. Daga nan kuma muka zaga sai ga mu a Rigiyum. Da muka kwana, iska ta taso daga kudu, kashegari kuma muka kai Butiyoli.

14. A nan muka tarar da waɗansu 'yan'uwa, suka roƙe mu mu kwana bakwai tare da su. Da haka dai har muka isa Roma.

15. Da 'yan'uwa na can suka ji labarinmu, sai da suka zo don su tarye mu har Kasuwar Abiyus, da kuma wurin nan da ake kira Maciya Uku. Da kuwa Bulus ya sadu da su, ya yi godiya ga Allah, jikinsa kuma ya yi ƙarfi.

16. Da muka shiga Roma aka yardar wa Bulus ya je ya sauka abinsa tare da sojan da yake tsaronsa.

17. Bayan kwana uku ya kira manyan Yahudawan birnin. Da suka taru sai ya ce musu, “Ya ku 'yan'uwa, ko da yake ban yi wa jama'armu wani laifi ba, ko laifi a game da al'adun kakanninmu, duk da haka an bashe ni ɗaurarre ga Romawa tun daga Urushalima.

18. Su kuwa da suka tuhume ni, suna so su sake ni, don ban yi wani laifi da ya isa kisa ba.

19. Amma da Yahudawa suka ƙi yarda, sai ya zamar mini dole in nema a ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar, ba don ina ƙarar jama'armu ba ne.

20. Shi ya sa na nema in gana da ku, tun da yake dai saboda sa zuciyar nan da Isra'ila take yi ne nake ɗaure da sarƙan nan.”

21. Sai suka ce masa, “Mu kam, ba mu sami wata wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, ba kuwa wani ɗan'uwanmu da ya zo nan ya kawo labarinka, ko yă faɗi wata mummunar magana game da kai.

22. Amma muna so mu ji daga bakinka abin da yake ra'ayinka, don in dai ta ɗariƙar nan ne, mun sani ko'ina ana kushenta.”

23. Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa'an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.

24. Waɗansu sun rinjayu da maganarsa, amma waɗansu sun ƙi gaskatawa.