Littafi Mai Tsarki

A.m. 22:20-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sa'ad da kuma aka zub da jinin Istifanas, mashaidin nan naka, ni ma ina a tsaye a gun, ina goyon bayan abin da aka yi, har ma ina tsare tufafin masu kisansa.’

21. Sai ya ce mini, ‘Tashi ka tafi, zan aike ka can nesa a wurin al'ummai.’ ”

22. Suna ta sauraronsa har ya iso kalmar nan, sai suka ɗau ihu suka ce, “A kashe shi! A raba irin mutumin nan da duniya, bai kyautu ya rayu ba!”

23. Da suka dinga ihu suna kaɗa mayafansu suna ta ature da ƙura,

24. sai shugaba ya yi umarni a kai Bulus kagarar soja a tuhume shi da bulala, don yă san abin da ya sa suke masa ihu haka.

25. Bayan sun ɗaɗɗaure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa jarumin ɗin da yake tsaye kusa, “Ashe, ya halatta a gare ka ka yi wa mutumin da yake da 'yancin Roma bulala, ba ko bin ba'asi?”

26. Da jarumin ɗin ya ji haka, sai ya je ya shaida wa shugaban, ya ce, “Me kake shirin yi ne? Mutumin nan fa Barome ne.”

27. Sai shugaban ya zo ya ce wa Bulus, “Faɗa mini gaskiya, kai kuwa Barome ne?” Sai ya ce, “I”.

28. Sai shugaban ya amsa ya ce, “Ni fa da kuɗi masu yawa na sami 'yancin nan.” Bulus ya ce, “ni kuwa da shi aka haife ni.”

29. Saboda haka, waɗanda suke shirin tuhumarsa, suka rabu da shi nan da nan. Shi ma shugaban da ya fahimci Bulus Barome ne, sai ya tsorata, ga shi kuwa, ya ɗaure shi.