Littafi Mai Tsarki

A.m. 2:34-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Ai, ba Dawuda ne ya hau Sama ba, amma shi kansa ya ce,‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,Zauna a damana,

35. Sai na sa ka take maƙiyanka.’

36. “Don haka sai duk jama'ar Isra'ila su sakankance, cewa shi Yesun na da kuka gicciye, Allah ya mai da shi Ubangiji, da kuma Almasihu.”

37. To, da suka ji haka, maganar ta soke su a zuci, suka ce wa Bitrus da sauran manzannin, “'Yan'uwa, me za mu yi?”

38. Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa ko wannenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki,

39. domin alkawarin nan ku aka yi wa, ku da 'ya'yanku, da kuma dukan manisanta, wato duk waɗanda Ubangiji Allahnmu ya kira.”

40. Sai ya yi ta tabbatar musu da maganganu masu yawa, yana ta yi musu gargaɗi, yana cewa, “Ku tsirar da kanku daga wannan karkataccen zamani.”

41. Waɗanda suka ya na'am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku.

42. Sai suka himmantu ga koyarwar manzanni da tarayya da juna, da gutsuttsura gurasa, da kuma yin addu'a.

43. Sai tsoro ya kama kowa, aka kuma yi abubuwan al'ajabi da mu'ujizai da yawa ta wurin manzannin.

44. Dukan masu ba da gaskiya suna tare, suna mallakar kome nasu gaba ɗaya.

45. Suka sayar da mallakarsu da kayansu, suka rarraba wa kowa kuɗin, gwargwadon bukatarsa.