Littafi Mai Tsarki

A.m. 13:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Shawulu kuwa, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya zuba masa ido,

10. ya ce, “Kai babban maha'inci, munafiƙi, ɗan Iblis, magabcin adalci duka, ba za ka daina karkata miƙaƙƙun hanyoyin Ubangiji ba?

11. To, ga shi, hannun Ubangiji na kanka, za ka makance, ba za ka ga rana ba har wani lokaci.” A nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi, ya yi ta neman wanda zai yi masa jagora.

12. Da muƙaddashin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, yana mamaki da koyarwar Ubangiji.

13. Sai Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafusa a jirgin ruwa, suka isa Bariyata ta ƙasar Bamfiliya. Yahaya kuwa ya bar su, ya koma Urushalima.

14. Amma suka wuce gaba daga Bariyata, suka tafi Antakiya ta ƙasar Bisidiya. Ran Asabar kuma sai suka shiga majami'a suka zauna.

15. Bayan an yi karatun Attaura da littattafan annabawa, shugabannin majami'ar suka aika musu, suka ce, “'Yan'uwa, in kuna da wata maganar gargaɗi da za ku yi wa jama'a, ai, sai ku yi.”

16. Sai Bulus ya miƙe, ya ɗaga hannu a yi shiru, ya ce,“Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, da sauran masu tsoron Allah, ku saurara!

17. Allahn jama'ar nan Isra'ila ya zaɓi kakanninmu, ya ɗaukaka jama'ar sa'ad da suke baƙunci a ƙasar Masar, da maɗaukakin iko kuma ya fito da su daga cikinta.