Littafi Mai Tsarki

A.m. 13:45-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

45. Amma da Yahudawa suka ga taro masu yawa, suka yi kishi gaya, suka yi ta musun abubuwan da Bulus ya faɗa, suna zaginsa.

46. Sai Bulus da Barnaba suka yi magana gabagaɗi, suka ce, “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da yake kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al'ummai.

47. Domin haka ubangiji ya umarce mu, ya ce,‘Na sa ka haske ga al'ummai,Don ka zama sanadin ceto, har ya zuwa iyakar duniya.’ ”

48. Da al'ummai suka ji haka, suka yi farin ciki, suka ɗaukaka Maganar Ubangiji, ɗaukacin kuma waɗanda aka ƙaddara wa samun rai madawwami suka ba da gaskiya.

49. Maganar Ubangiji kuwa, sai ta yi ta yaɗuwa a duk ƙasar.

50. Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu ibada, masu daraja, da kuma waɗansu manyan gari, suka haddasa tsanani ga Bulus da Barnaba, suka kore su daga ƙasarsu.

51. Su kuwa suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaida a kansu, suka tafi Ikoniya.

52. Amma kuwa masu bi suna farin ciki matuƙa, suna kuma a cike da Ruhu Mai Tsarki.