Littafi Mai Tsarki

A.m. 13:32-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Mu ma mun kawo muku albishir, cewa, alkawarin nan da Allah ya yi wa kakanninmu,

33. ya cika mana shi, mu zuriyarsu, da ya ta da Yesu daga matattu, yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa,‘Kai Ɗana ne,Ni Ubanka ne yau.’

34. Game da ta da shi daga matattu da Allah ya yi, a kan cewa ba zai sāke komawa cikin halin ruɓa ba kuwa, ga abin da ya ce,‘Zan yi muku tsattsarkar albarkar nan da na tabbatar wa Dawuda.’

35. Domin a wata Zabura ma ya ce,‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’

36. Dawuda kam, bayan da ya bauta wa mutanen zamaninsa bisa ga nufin Allah, ya yi barci, aka binne shi tare da kakanninsa, ya kuwa ruɓe.

37. Amma shi wannan da Allah ya tashe shi, bai ruɓa ba.

38. Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku sani albarkacin mutumin nan ne ake sanar da ku gafarar zunubanku.

39. Ta gare shi kuma, duk masu ba da gaskiya suka kuɓuta daga dukan abubuwan da ba dama Shari'ar Musa ta kuɓutar da ku.

40. Saboda haka sai ku mai da hankali, kada abin nan da littattafan annabawa suke faɗa ya aukar muku, wato

41. ‘Ga shi, ku masu rainako,Za ku ruɗe don mamaki, ku shuɗe!Domin zan yi wani aiki a zamaninku,Aikin da ba yadda za a yi ku gaskata,Ko da wani ya gaya muku.’ ”

42. Suna fita majami'a ke nan, sai mutane suka roƙe su su ƙara yi musu wannan magana a ran Asabar mai zuwa.

43. Da jama'a suka watse, Yahudawa da yawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, masu ibada, suka bi Bulus da Barnaba. Su kuma suka yi musu magana, suna yi musu gargaɗi su zauna a cikin alherin Allah.

44. Da Asabar ta kewayo, kusan duk birnin, suka hallara su ji Maganar Allah.

45. Amma da Yahudawa suka ga taro masu yawa, suka yi kishi gaya, suka yi ta musun abubuwan da Bulus ya faɗa, suna zaginsa.

46. Sai Bulus da Barnaba suka yi magana gabagaɗi, suka ce, “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da yake kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al'ummai.

47. Domin haka ubangiji ya umarce mu, ya ce,‘Na sa ka haske ga al'ummai,Don ka zama sanadin ceto, har ya zuwa iyakar duniya.’ ”