Littafi Mai Tsarki

A.m. 13:11-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. To, ga shi, hannun Ubangiji na kanka, za ka makance, ba za ka ga rana ba har wani lokaci.” A nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi, ya yi ta neman wanda zai yi masa jagora.

12. Da muƙaddashin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, yana mamaki da koyarwar Ubangiji.

13. Sai Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafusa a jirgin ruwa, suka isa Bariyata ta ƙasar Bamfiliya. Yahaya kuwa ya bar su, ya koma Urushalima.

14. Amma suka wuce gaba daga Bariyata, suka tafi Antakiya ta ƙasar Bisidiya. Ran Asabar kuma sai suka shiga majami'a suka zauna.

15. Bayan an yi karatun Attaura da littattafan annabawa, shugabannin majami'ar suka aika musu, suka ce, “'Yan'uwa, in kuna da wata maganar gargaɗi da za ku yi wa jama'a, ai, sai ku yi.”

16. Sai Bulus ya miƙe, ya ɗaga hannu a yi shiru, ya ce,“Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, da sauran masu tsoron Allah, ku saurara!

17. Allahn jama'ar nan Isra'ila ya zaɓi kakanninmu, ya ɗaukaka jama'ar sa'ad da suke baƙunci a ƙasar Masar, da maɗaukakin iko kuma ya fito da su daga cikinta.

18. Wajen shekara arba'in yake haƙuri da su cikin jeji.

19. Ya kuma hallaka al'umma bakwai a ƙasar Kan'ana, sai ya raba musu ƙasar tasu gādo, suka zauna har shekara arbaminya da hamsin.

20. Bayan haka kuma ya naɗa musu mahukunta har ya zuwa zamanin Annabi Sama'ila.

21. Sa'an nan suka roƙa a naɗa musu sarki, sai Allah ya ba su Saul ɗan Kish, mutumin kabilar Biliyaminu, har shekara arba'in.

22. Bayan da ya kawar da shi sai ya gabatar da Dawuda ya zama sarkinsu, ya kuma shaide shi da cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake ƙauna ƙwarai, wanda kuma zai aikata dukan nufina.’

23. Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra'ila Mai Ceto, Yesu kamar yadda ya yi alkawari.

24. Kafin ya bayyana a fili kuwa, Yahaya ya yi wa duk jama'ar Isra'ila wa'azi su tuba a kuma yi musu baftisma.

25. Yayin da Yahaya ya kusa gama nasa zamani, sai ya ce, ‘Wa kuke tsammani nake? Ba fa ni ne shi ɗin nan ba. Amma ga shi akwai wani mai zuwa a bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in balle ba.’