Littafi Mai Tsarki

Zab 21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Yabo saboda Nasara

1. Sarki yana murna, ya Ubangiji,Domin ka ba shi ƙarfi,Yana cike da farin ciki,Don ka sa ya ci nasara.

2. Ka biya masa bukatarsa,Ka amsa roƙonsa.

3. Ka zo gare shi da albarka mai yawa,Ka sa kambin zinariya a kansa.

4. Ya roƙi rai, ka kuwa ba shi mai tsawo,Da yawan kwanaki.

5. Darajarsa tana da girma saboda taimakonka,Ka sa ya yi suna da martaba.

6. Albarkarka tana a kansa har abada,Kasancewarka tare da shi, takan cika shi da murna.

7. Sarki yana dogara ga Maɗaukaki,Saboda madawwamiyar ƙaunar UbangijiZai zama sarki har abada.

8. Sarki zai kakkama dukan magabtansa,Zai kakkama duk waɗanda suke ƙinsa.

9. Ubangiji zai hallaka su kamar harshen wuta, sa'ad da ya bayyana.Ubangiji zai cinye su a cikin fushinsa,Wuta kuma za ta cinye su ƙurmus.

10. Sarki zai karkashe 'ya'yansu duka,Zai yanyanke dukan zuriyarsu.

11. Sun ƙulla mugayen dabaru, suna fakonsa,Amma ba za su yi nasara ba.

12. Zai harba kibansa a kansu,Ya sa su juya su gudu.

13. Ya Ubangiji, ka zo da ƙarfinka!Za mu raira waƙa mu yabi ikonka.