Littafi Mai Tsarki

Zab 131 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Addu'ar Tawali'u

1. 'Ya Ubangiji, na rabu da girmankai,Na bar yin fariya,Ba ruwana da manyan al'amura,Ba ruwana kuma da zantuttukan da suka fi ƙarfina.

2. Amma na haƙura, raina a kwance,Kamar jinjirin da yake kwance jalisan a hannun mahaifiyarsa,Haka zuciyata take kwance.

3. Ya Isra'ila, ka dogara ga Ubangiji,Daga yanzu har abada!