Littafi Mai Tsarki

Zab 100 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Waƙar Yabo

1. Bari dukan duniya ta raira waƙar farin ciki ga Ubangiji!

2. Ku yi wa Ubangiji sujada da murna,Ku zo gabansa, kuna raira waƙoƙin farin ciki!

3. Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Allah!Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne,Mu jama'arsa ne, mu garkensa ne.

4. Ku shiga Haikalinsa da godiya,Ku shiga wurinsa mai tsarki, ku yabe shi!Ku gode masa, ku yabe shi!

5. Ubangiji nagari ne,Ƙaunarsa madawwamiya ce,Amincinsa kuwa har abada abadin ne.