Littafi Mai Tsarki

Zab 99:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji Sarki ne,Mutane suna rawar jiki,Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi,Duniya ta girgiza.

2. Ubangiji mai iko ne a Sihiyona,Shi ne yake mulki a bisa dukan sauran al'umma.

3. Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, MaÉ—aukaki,Mai Tsarki ne shi!