Littafi Mai Tsarki

Zab 96:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji!Ku raira waƙa ga Ubangiji, ya duniya duka!

2. Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku yabe shi!Kowace rana ku ba da labari mai daɗi cewa,“Ya cece mu!”

3. Ku yi shelar ɗaukakar Ubangiji ga sauran al'umma,Ku yi shelar ayyukansa masu girma ga dukan kabilai.

4. Ubangiji da girma yake, tilas a ɗaukaka shi,Tilas a fi jin tsoronsa fiye da dukan alloli.

5. Allolin dukan al'ummai, gumaka ne kawai,Amma Ubangiji ne ya yi sammai.

6. Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi,Girma da jamali suna cikin Haikalinsa.

7. Dukan jama'ar da suke bisa duniya su yabi Ubangiji!Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!

8. Ku yabi sunan Ubangiji mai ɗaukaka,Ku kawo sadaka, ku shiga Haikalinsa.