Littafi Mai Tsarki

Zab 94:10-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Shi ne yake shugabancin sauran al'umma, ba zai hukunta su ba?Shi ne yake koya wa dukan mutane, shi ba shi da sani ne?

11. Ubangiji ya san tunaninsu,Ya san kuma hujjojinsu na rashin hankali.

12. Ya Ubangiji, mai farin ciki ne mutumin da kake koya wa,Mutumin da kake koya masa shari'arka.

13. Don ka ba shi hutawa a kwanakin wahala,Kafin a haƙa wa mugaye kabari.

14. Ubangiji ba zai rabu da jama'arsa ba,Ba zai rabu da waɗanda suke nasa ba.

15. Adalci kuma zai sāke dawowa cikin majalisun alƙalai,Dukan adalai kuwa za su yi na'am da shi.

16. Wa zai tsaya mini gāba da mugaye?Wa zai goyi bayana gāba da masu aikata mugunta?

17. Da ba domin Ubangiji ya taimake ni ba,Ai, da tuni na kai ƙasar da ba a motsi.

18. Na ce, “Ina kan fāɗuwa,”Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni.

19. Sa'ad da nake alhini, ina cikin damuwa,Ka ta'azantar da ni, ka sa in yi murna.

20. Ba ruwanka da alƙalai azzalumai, marasa gaskiya,Waɗanda suka mai da rashin gaskiya ita ce gaskiyarsu,

21. Sukan shirya wa mutanen kirki maƙarƙashiya,Sukan yanke wa marar laifi hukuncin kisa.

22. Amma Ubangiji yakan kāre ni,Allahna yakan kiyaye ni.