12. Adalai za su yi yabanyaKamar itatuwan giginya,Za su yi girma kamar itatuwan al'ul na Lebanon.
13. Za su zama kamar itatuwan da aka daddasa a Haikalin Ubangiji,Suna ta yabanya a Haikalin Allahnmu.
14. Waɗanda suke yin 'ya'ya da tsufansu,A kullum kuwa kore shar suke,Suna da ƙarfinsu kuma.
15. Wannan ya nuna Ubangiji adali ne,Shi wanda yake kāre ni,Ba kuskure a gare shi.