Littafi Mai Tsarki

Zab 9:18-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ba kullum ne ake ƙyale masu bukata ba,Ba za a danne sa zuciyar waɗanda ake zalunta ba har abada.

19. Ka zo, ya Ubangiji! Kada ka bari mutane su gagare ka!Ka kawo arna a gabanka, ka hukunta su.

20. Ka sa su ji tsoro, ya Ubangiji,Ka sa su sani su mutane ne kawai.