Littafi Mai Tsarki

Zab 9:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji,Zan hurta dukan abubuwa masu banmamaki da ka yi.

2. Zan raira waƙa da farin ciki sabili da kai,Zan raira yabo gare ka, ya Maɗaukaki!

3. Magabtana sun jā da baya da suka gan ka,Suka faɗi, suka mutu.