Littafi Mai Tsarki

Zab 89:30-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. “Amma idan zuriyarsa sun ƙi yin biyayya da shari'ata,Ba su kuwa zauna cikin ka'idodina ba,

31. In sun ƙyale koyarwata,Ba su kiyaye umarnaina ba,

32. To, sai in hukunta su saboda zunubansu,Zan bulale su saboda laifofinsu.

33. Amma fa, ba zan daina ƙaunar Dawuda ba,Ba kuwa zan rasa cika alkawarin da na yi masa ba.

34. Ba zan keta alkawarin da na yi masa ba,Ba zan soke ko ɗaya daga cikin alkawaran da na yi masa ba.

35. “Da sunana mai tsarki na yi alkawari sau ɗaya tak,Ba zan yi wa Dawuda ƙarya ba!

36. Zuriyarsa za ta kasance kullum,Zan lura da mulkinsa muddin rana tana haskakawa.

37. Zai dawwama kamar wata,Kamar amintaccen mashaidin nan da yake a sararin sama.”

38. Amma kana fushi da zaɓaɓɓen sarkinka,Ka rabu da shi, ka yashe shi.

39. Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka,Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.