Littafi Mai Tsarki

Zab 89:29-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. A kullayaumin daga cikin zuriyarsa ne za a naɗa sarki,Mulkinsa zai dawwama kamar sararin sama.

30. “Amma idan zuriyarsa sun ƙi yin biyayya da shari'ata,Ba su kuwa zauna cikin ka'idodina ba,

31. In sun ƙyale koyarwata,Ba su kiyaye umarnaina ba,

32. To, sai in hukunta su saboda zunubansu,Zan bulale su saboda laifofinsu.

33. Amma fa, ba zan daina ƙaunar Dawuda ba,Ba kuwa zan rasa cika alkawarin da na yi masa ba.