Littafi Mai Tsarki

Zab 88:15-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Tun ina ƙarami nake shan wahala,Har ma na kusa mutuwa,Na tafke saboda nauyin hukuncinka.

16. Hasalarka ta bi ta kaina,Tasar mini da kake ta yi, ta hallaka ni.

17. Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa,Ta kowace fuska, sun rufe ni.

18. Ka sa har abokaina na kusa sun yashe ni,Duhu ne kaɗai abokin zamana.