Littafi Mai Tsarki

Zab 81:11-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. “Amma jama'ata ba su kasa kunne gare ni ba.Isra'ila ta ƙi yi mini biyayya.

12. Saboda haka na bar su su yi ta kangarewarsu,Su aikata duk irin abin da suka ga dama.

13. Ina kuwa so jama'ata su kasa kunne gare ni,Su kuwa yi mini biyayya!

14. Da sai in kori abokan gābansu nan da nan,In yi nasara da dukan maƙiyansu.

15. Maƙiyana, za su sunkuya a gabana saboda tsoro,Hukuncinsu na har abada ne.

16. Zan ciyar da ku da kyakkyawar alkama,In ƙosar da ku da zuma.”