Littafi Mai Tsarki

Zab 8:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, Ubangijinmu,An san girmanka ko'ina a dukan duniya.Yabonka ya kai har sammai,

2. Yara da jarirai suna raira shi,Ka gina kagara saboda magabtanka,Domin ka tsai da maƙiyanka da abokan gābanka.

3. Sa'ad da na duba sararin sama, wanda ka yi,Da wata da taurari waɗanda ka sa a wuraren zamansu,

4. Wane ne mutum, har da kake tunawa da shi,Mutum kurum, har da kake lura da shi?

5. Duk da haka in banda kai ba wanda ya fi shi,Ka naɗa shi da daraja da girma!

6. Ka sa shi ya yi mulkin dukan abin da ka halitta,Ka ɗora shi a kan dukan abubuwa,