Littafi Mai Tsarki

Zab 79:11-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ka kasa kunne ga nishin 'yan sarƙa,Ka kuɓutar da waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa,Ta wurin ikonka mai girma.

12. Ya Ubangiji, ka rama wa al'umman nan har sau bakwai,Saboda tsiwace-tsiwacen da suka yi maka.

13. Mu waɗanda muke jama'arka, tumakin garkenka,Za mu gode maka, mu yabe ka har abada.