Littafi Mai Tsarki

Zab 78:31-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Sai Allah ya yi fushi da su.Ya karkashe ƙarfafan mutane,Da samarin Isra'ila na gaske!

32. Ko da yake ya aikata mu'ujizai da yawa,Duk da haka jama'a suka ci gaba da yin zunubi,Ba su kuwa gaskata shi ba.

33. Ta haka ya ƙare kwanakinsu kamar fitar numfashi,Bala'i ya aukar wa rayukansu farat ɗaya.

34. Amma sa'ad da ya kashe waɗansunsu,Sai sauran suka juyo gare shi suka tuba,Suka yi addu'a sosai a gare shi.

35. Sun tuna, ashe, Allah ne mai kiyaye su,Sun tuna Maɗaukaki shi ne Mai Fansarsu.

36. Amma maganganunsu duka ƙarya ne,Dukan abin da suka faɗa kuwa daɗin baki ne kawai.