Littafi Mai Tsarki

Zab 78:28-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Sai suka fāɗo a zango,Kewaye da alfarwai ko'ina.

29. Sai mutane suka ci suka ƙoshi,Allah ya ba su iyakar abin da suke bukata.

30. Amma sa'ad da suke cikin ci,Tun ba su ƙoshi ba,

31. Sai Allah ya yi fushi da su.Ya karkashe ƙarfafan mutane,Da samarin Isra'ila na gaske!