Littafi Mai Tsarki

Zab 77:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Allah ya manta da yin jinƙai ne?Fushinsa ya maye matsayin juyayinsa ne?

10. Sa'an nan sai na ce, “Abin da ya fi mini zafi duka,Shi ne ikon Maɗaukaki ya ragu.”

11. Zan tuna da manyan ayyukanka, ya Ubangiji,Zan tuna da al'amura masu banmamaki da ka aikata a dā.

12. Zan tuna da dukan abubuwan da ka yi,Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka.

13. Dukan abin da kake yi mai tsarki ne, ya Allah!Ba wani allah mai girma kamarka!

14. Kai ne Allah wanda kake aikata al'ajabai,Ka nuna ikonka cikin sauran al'umma.

15. Ta wurin ikonka ka fanshi jama'arka,Zuriyar Yakubu da ta Yusufu.

16. Ya Allah, sa'ad da ruwaye suka gan ka, sai su tsorata,Zurfafan teku kuma suka yi rawar jiki.

17. Gizagizai suka zubo da ruwa,Aka buga tsawa daga sama,Aka kuwa yi walƙiya ko'ina.

18. Bugawar tsawarka ta gama ko'ina,Hasken walƙiya ya haskaka dukan duniya,Duniya ta yi rawa, ta girgiza, ta kaɗu.

19. Ka yi tafiya a teku,Ka haye teku mai zurfi,Amma ba a ga shaida inda ka taka ba.

20. Ka bi da jama'arka yadda makiyayi yake yi,Musa da Haruna suke lura da su.