Littafi Mai Tsarki

Zab 77:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ba ya barina in yi barci,Na damu har na kāsa magana.

5. Na yi tunanin kwanakin da suka wuce,Nakan kuma tuna da shekarun da suka wuce da daɗewa.

6. Dare farai ina ta tunani mai zurfi,A cikin tunani nakan yi wa kaina tambaya.

7. A kullum ne Ubangiji zai yashe ni?Ba kuma zai ƙara yin murna da ni ba?