Littafi Mai Tsarki

Zab 77:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na ta da murya, na yi kuka ga Allah,Na ta da murya, na yi kuka, ya kuwa ji ni.

2. A lokacin wahala, nakan yi addu'a ga Ubangiji,Dukan dare nakan ɗaga hannuwana sama in yi addu'a,Amma ban sami ta'aziyya ba.

3. Lokacin da na tuna da Allah na yi ajiyar zuciya.Sa'ad da nake tunani,Nakan ji kamar in fid da zuciya.

4. Ba ya barina in yi barci,Na damu har na kāsa magana.

5. Na yi tunanin kwanakin da suka wuce,Nakan kuma tuna da shekarun da suka wuce da daɗewa.

6. Dare farai ina ta tunani mai zurfi,A cikin tunani nakan yi wa kaina tambaya.

7. A kullum ne Ubangiji zai yashe ni?Ba kuma zai ƙara yin murna da ni ba?

8. Ya daina ƙaunata ke nan?Alkawarinsa ba shi da wani amfani?

9. Allah ya manta da yin jinƙai ne?Fushinsa ya maye matsayin juyayinsa ne?

10. Sa'an nan sai na ce, “Abin da ya fi mini zafi duka,Shi ne ikon Maɗaukaki ya ragu.”

11. Zan tuna da manyan ayyukanka, ya Ubangiji,Zan tuna da al'amura masu banmamaki da ka aikata a dā.

12. Zan tuna da dukan abubuwan da ka yi,Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka.

13. Dukan abin da kake yi mai tsarki ne, ya Allah!Ba wani allah mai girma kamarka!

14. Kai ne Allah wanda kake aikata al'ajabai,Ka nuna ikonka cikin sauran al'umma.