Littafi Mai Tsarki

Zab 74:15-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ka sa ruwan maɓuɓɓugai ya yi gudu,Ka sa manyan koguna su ƙafe.

16. Ka halicci yini da dare,Ka sa rana da wata a wurarensu.

17. Ka yi wa duniya kan iyaka,Ka kuwa yi lokatan damuna da na rani.

18. Amma ka tuna fa, ya Ubangiji, abokan gābanka suna yi maka ba'a,Su wawaye ne waɗanda suke raina ka.