Littafi Mai Tsarki

Zab 73:3-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Saboda na ji kishin masu girmankai,Sa'ad da na ga mugaye suna arziki.

4. Ba su jin zafin ciwo,Su ƙarfafa ne, lafiyayyu.

5. Ba su shan wahala yadda sauran mutane suke sha,Ba su da wahala kamar sauran mutane,

6. Don haka suka ɗaura girmankai kamar dutsen wuya,Suka sa hargitsi kuma kamar riga.

7. Zuciyarsu, cike take da mugunta,Tunaninsu kuma cike suke da mugayen ƙulle-ƙulle.

8. Sukan yi wa waɗansu ba'a,Suna faɗar mugayen abubuwa,Masu girmankai ne su, suna shawaraA kan yadda za su zalunci waɗansu.

9. Sukan faɗi baƙar magana a kan Allah na Sama,Su ba da umarnai na girmankai ga mutane a duniya,

10. Har jama'ar Allah ma sukan koma wurinsu,Suna ɗokin gaskata dukan abin da suke faɗa musu.

11. Sukan ce, “Ai, Allah ba zai sani ba,Maɗaukaki ba zai bincika ba!”

12. Haka mugaye suke.Suna da dukiya da yawa, amma sai ƙaruwa suke ta yi.

13. Ashe, a banza nake kiyaye kaina da tsarki,Hannuwana kuma a tsabtace daga zunubi?

14. Ya Allah, ka sa ina shan wahala dukan yini,Kana horona kowace safiya!