Littafi Mai Tsarki

Zab 73:24-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Shawararka, tana bi da ni,Daga ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja.

25. In banda kai, wa nake da shi a Sama?Tun da yake ina da kai, me kuwa nake bukata a duniya?

26. Kwanyata da jikina za su raunana,Amma Allah ne ƙarfina,Shi nake so har abada!