Littafi Mai Tsarki

Zab 73:18-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Hakika ka sa su a wurare masu santsi,Ka sa su su fāɗi su hallaka sarai!

19. Cikin ƙyaftawar ido aka hallaka su,Suka yi mummunan ƙarshe!

20. Ya Ubangiji, kamar mafarki sukeWanda akan manta da shi da safe,Sa'ad da mutum ya farka yakan manta da kamanninsa.

21. Sa'ad da zuciyata ta ɓaci,Hankalina ya tashi,