Littafi Mai Tsarki

Zab 73:14-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ya Allah, ka sa ina shan wahala dukan yini,Kana horona kowace safiya!

15. Da na faɗi waɗannan abubuwa,Da na zama marar gaskiya ga jama'arka.

16. Don haka na yi iyakar ƙoƙari in fahimci wannan,Ko da yake ya cika wuya,

17. Sai sa'ad da na shiga Haikalinka,Sa'an nan na fahimci abin da zai sami mugaye.

18. Hakika ka sa su a wurare masu santsi,Ka sa su su fāɗi su hallaka sarai!

19. Cikin ƙyaftawar ido aka hallaka su,Suka yi mummunan ƙarshe!

20. Ya Ubangiji, kamar mafarki sukeWanda akan manta da shi da safe,Sa'ad da mutum ya farka yakan manta da kamanninsa.

21. Sa'ad da zuciyata ta ɓaci,Hankalina ya tashi,

22. Sai na zama wawa, ban fahimta ba,Na nuna halin dabba a gabanka.

23. Duk da haka ina tare da kai kullayaumin,Kana riƙe da hannuna.

24. Shawararka, tana bi da ni,Daga ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja.

25. In banda kai, wa nake da shi a Sama?Tun da yake ina da kai, me kuwa nake bukata a duniya?

26. Kwanyata da jikina za su raunana,Amma Allah ne ƙarfina,Shi nake so har abada!

27. Hakika waɗanda za su rabu da kai za su mutu,Za ka hallakar da marasa aminci gare ka.

28. Amma a gare ni, ya fi mini kyau, in kasance kusa da Allah!Na sami mafaka a wurin Ubangiji Allah,Da zan yi shelar dukan abin da ya aikata.