Littafi Mai Tsarki

Zab 71:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Raina abin damuwa ne ga mutane da yawa,Amma kai ne kāriyata mai ƙarfi.

8. Ina yabonka dukan yini,Ina shelar darajarka.

9. Yanzu da na tsufa, kada ka yashe ni,Yanzu da ƙarfina ya ƙare kuma, kada ka rabu da ni!

10. Maƙiyana, waɗanda suke so su kashe ni,Suna magana, suna ƙulle-ƙulle gāba da ni.

11. Suna cewa, “Ai, Allah ya rabu da shi,Gama ba wanda zai cece shi!”

12. Kada ka yi nisa da ni haka, ya Allah,Ka yi hanzari ka taimake ni, ya Allahna!

13. Ka sa a kori waɗanda suka tasar mini,A hallaka su!Ka sa a kunyata waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni,A wulakanta su sarai!

14. A koyaushe zan sa zuciya gare ka,Zan yi ta yabonka.