Littafi Mai Tsarki

Zab 69:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Waɗanda suke ƙina ba daliliSun fi gashin kaina yawa,Waɗanda suke baza ƙarya suke ƙina,Suna da ƙarfi, suna kuwa so su kashe ni.Suka tilasta ni in mayar da abubuwan da ba satarsu na yi ba.

5. Zunubaina ba a ɓoye suke a gare ka ba ya Allah,Ka san irin wawancin da na yi!

6. Kada ka bar ni in jawo kunya ga waɗanda suka dogara gare ka,Ya Ubangiji Allah Mai Iko Dukka!Kada ka bar ni in jawo abin kunyaGa waɗanda suke maka sujada, ya Allah na Isra'ila!

7. Sabili da kai ne aka ci mutuncina,Kunya ta rufe ni.

8. Kamar baƙo nake ga 'yan'uwana,Haka ma ga iyalina, kamar baƙo nake.