Littafi Mai Tsarki

Zab 69:26-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Sun tsananta wa waɗanda ka hukunta,Suna taɗin shan wuyar waɗanda ka aukar wa cutar.

27. Ka riɓaɓɓanya zunubansu,Kada ka bar su su sami rabon kome daga cikin cetonka.

28. Ka sa a goge sunansu daga cikin littafin rai,Kada a sa su a lissafin jama'arka.

29. Amma ni mai bukata ne, ina shan wahala,Ka tsame ni, ya Allah, ka cece ni!

30. Zan raira waƙar yabo ga Allah,Zan yi shelar girmansa ta wurin yi masa godiya,

31. Wannan zai daɗaɗa wa Ubangiji raiFiye da hadayar bijimi,Fiye da a ba shi bijimi bana bakwai.

32. Sa'ad da masu bukata suka ga wannan za su yi murna,Waɗanda suke yi wa Allah sujada kuwa za a ƙarfafa su.

33. Ubangiji yana kasa kunne ga masu bukata,Bai manta da jama'arsa da suke a kurkuku ba.

34. Ku yabi Allah, ku al'arshi da duniya, ku yabi Allah,Tekuna da dukan talikan da suke cikinsu!

35. Gama zai ceci Sihiyona,Ya sāke gina garuruwan Yahuza,Jama'arsa za su zauna a wurin, su mallaki ƙasar.

36. Zuriyar bayinsa za su gāje ta,Masu ƙaunarsa za su zauna a wurin.