Littafi Mai Tsarki

Zab 69:19-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Ka san yadda ake cin mutuncina,Da yadda ake kunyata ni, ake ƙasƙantar da ni,Kana ganin dukan abokan gābana.

20. Zuciyata ta karai saboda cin mutuncin da ake ci mini,Ni kuwa ba ni da mataimaki,Na sa zuciya za a kula da ni,Amma babu.Na sa zuciya zan sami ta'aziyya,Amma ban samu ba.

21. Sa'ad da na ji yunwa, sai suka ba ni dafi,Sa'ad da na ji ƙishi, sai suka ba ni ruwan tsami.

22. Allah ya sa bukukuwansu su zama lalacewarsu,Shagulgulansu kuma su zama sanadin fāɗuwarsu!

23. Ka makantar da su, har da ba za su iya gani ba,Kullum ka sa bayansu ya ƙage!

24. Ka kwarara musu fushinka,Bari zafin fushinka ya ci musu!

25. Allah ya sa su gudu su bar sansaninsu,Kada wani ya ragu da rai cikin alfarwansu!

26. Sun tsananta wa waɗanda ka hukunta,Suna taɗin shan wuyar waɗanda ka aukar wa cutar.

27. Ka riɓaɓɓanya zunubansu,Kada ka bar su su sami rabon kome daga cikin cetonka.

28. Ka sa a goge sunansu daga cikin littafin rai,Kada a sa su a lissafin jama'arka.