Littafi Mai Tsarki

Zab 68:8-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Duniya ta girgiza, sararin sama ya kwararo ruwa,Saboda bayyanar Allah, har Dutsen Sinai ya girgiza,Saboda bayyanar Allah na Isra'ila.

9. Ka sa aka yi ruwan sama mai yawa, ya Allah,Ka rayar da ƙasarka wadda ta zozaye.

10. Jama'arka suka gina gidajensu a can,Ta wurin alherinka ka yi wa matalauta tanadi.

11. Ubangiji ya ba da umarni,Sai mata masu yawa suka baza labari cewa,

12. “Sarakuna da rundunan sojojinsu suna gudu!Matan da suke a gida suka rarraba ganima.”

13. Suna kamar kurciyoyin da aka dalaye da azurfa,Waɗanda fikafikansu suna ƙyalli kamar kyakkyawar zinariya.(Me ya sa waɗansunku suke zaune cikin shingen tumaki?)

14. Sa'ad da Allah Mai Iko DukkaYa warwatsar da sarakuna a dutsen Zalmon,Sai ya sa dusar ƙanƙara ta sauka a wurin.

15. Wane irin babban dutse ne wannan dutsen Bashan?Tulluwarka nawa, dutsen Bashan?

16. Me ya sa, daga manyan kawunankaKake yi wa dutsen da Allah ya zaɓaYa zauna a kai, duban raini?A nan Ubangiji zai zauna har abada!

17. Daga Sinai da dubban manyan karusansa,Ubangiji ya zo tsattsarkan Haikalinsa.

18. Ya hau kan tsaunukaTare da ɗumbun waɗanda ya kamo daga yaƙi,Yana karɓar kyautai daga wurin mutane,Daga wurin 'yan tawaye kuma.Ubangiji Allah zai zauna a can.

19. Ku yabi Ubangiji,Wanda yake ɗaukar nawayarmu ta yau da kullum,Shi ne Allah wanda ya cece mu.

20. Allahnmu, Allah Mai Ceto ne,Shi ne Ubangiji, Ubangijinmu,Wanda yake cetonmu daga mutuwa.

21. Hakika Allah zai farfashe kawunan abokan gābansa,Da na waɗanda suka nace bin hanyoyinsu na zunubi.

22. Ubangiji ya ce, “Zan komo da su daga Bashan,Zan komo da su daga zurfin teku,