Littafi Mai Tsarki

Zab 68:31-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Wakilai za su zo daga Masar,Habashawa za su miƙa hannuwansu sama,Su yi addu'a ga Allah.

32. Ku raira waƙa ga Allah, ku mulkokin duniya,Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji,

33. Shi wanda ya hau cikin sararin sama,Daɗaɗɗen sararin sama!Ku kasa kunne ga muryarsa mai ƙarfi!

34. Ku yi shelar ikon Allah,Ɗaukakarsa tana bisa kan Isra'ila,Ikonsa yana cikin sararin sama.

35. Allah al'ajabi ne a tsattsarkan wurinsa,Allah na Isra'ila!Yana ba da ƙarfi da iko ga jama'arsa.Ku yabi Allah!