Littafi Mai Tsarki

Zab 68:15-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Wane irin babban dutse ne wannan dutsen Bashan?Tulluwarka nawa, dutsen Bashan?

16. Me ya sa, daga manyan kawunankaKake yi wa dutsen da Allah ya zaɓaYa zauna a kai, duban raini?A nan Ubangiji zai zauna har abada!

17. Daga Sinai da dubban manyan karusansa,Ubangiji ya zo tsattsarkan Haikalinsa.

18. Ya hau kan tsaunukaTare da ɗumbun waɗanda ya kamo daga yaƙi,Yana karɓar kyautai daga wurin mutane,Daga wurin 'yan tawaye kuma.Ubangiji Allah zai zauna a can.

19. Ku yabi Ubangiji,Wanda yake ɗaukar nawayarmu ta yau da kullum,Shi ne Allah wanda ya cece mu.