Littafi Mai Tsarki

Zab 61:2-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sa'ad da nake nesa da gida, zuciyata ta karai,Zan yi kira gare ka!Ka kai ni lafiyayyiyar mafaka.

3. Kai ne kāriyata mai ƙarfiDa take kiyaye ni daga maƙiyana.

4. Ka yarda in zauna a alfarwarka dukan kwanakin raina,Ka yarda in sami zaman lafiya a ƙarƙashin fikafikanka.

5. Ya Allah, kā ji alkawaraina,Kā kuwa ba ni abin da ya dace,Tare da waɗanda suke ɗaukaka ka.

6. Ka ƙara wa sarki tsawon rai,Ka sa ya rayu dukan lokaci!

7. Ka sa ya yi mulki har abada a gabanka, ya Allah,Ka tsare shi da madawwamiyar ƙaunarka, da amincinka.

8. Don haka zan yi ta raira waƙar yabonka kullayaumin,A sa'ad da nake miƙa maka abin da na alkawarta.