Littafi Mai Tsarki

Zab 60:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka rabu da mu, ya Allah, har aka ci nasara a kanmu,Ka yi fushi da mu, amma yanzu sai ka juyo wurinmu!

2. Ka sa ƙasar ta girgiza, ka tsaga ta.Yanzu sai ka warkar da tsaguwarta, gama tana gab da fāɗuwa!

3. Ka sa jama'arka su sha wahala ƙwarai,Ka ba mu ruwan inabin da ya bugar da mu.

4. Ka ta da tuta ga masu tsoronka,Domin su juya su gudu daga abokin gāba.

5. Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu'ata,Domin jama'ar da kake ƙauna ta sami cetonka.

6. A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce,“Da nasara zan raba Shekem,Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama'ata.