Littafi Mai Tsarki

Zab 6:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, kada ka yi fushi, ka kuma tsauta mini!Kada ka hukunta ni da fushinka!

2. Ka ji tausayina, gama na gaji tiƙis,Ka wartsarkar da ni, gama na tafke sarai.

3. Duk na damu ƙwarai da gaske.Sai yaushe wannan zai ƙare, ya Ubangiji?

4. Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni,Gama kana ƙaunata, ka kuɓutar da ni daga mutuwa.