Littafi Mai Tsarki

Zab 58:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Hakika za ku yanka daidai, ku manya?Za ku shara'anta wa mutane daidai?

2. A'a, tunanin muguntar da za ku aikata kaɗai kuke yi,Kuna aikata laifofin ta da hargitsi a ƙasar.

3. Mugaye, laifi suke yi dukan kwanakinsu,Tun daga ranar da aka haife su suke ta faɗar ƙarya.

4. Cike suke da dafi kamar macizai,Sukan toshe kunnuwansu kamar kuraman gamsheƙa,

5. Wanda ba ya jin muryar gardi,Ko kuma waƙar gwanin sihiri.

6. Ka kakkarya haƙoransu, ya Allah,Ka ciccire fiƙoƙin waɗannan zakoki masu zafin rai, ya Ubangiji!